Jami’an Nijar Sun Kama Yan Najeriya Uku Da Suka Hadiye Miyagun Kwayoyi Don Safararsu
Hakan na zuwa ne mako guda bayan da hukumar OCRTIS ta gano wani dan Najeriya ya yi amfani da irin wannan hanya wajen boye hodar iblis a duburarsa.

An gano hodar iblis da aka kukkulla cikin kororon roba kimanin 50 da mutanen uku suka hadiye da nufin safararsu zuwa kasar Aljeriya, a lokacin da suka isa shingen binciken masu shiga da fita. Jami’ai sun kwashe mutanen zuwa asibiti domin gudanar da bincike

A farkon makon jiya ma ‘yan sanda sun gabatar da wani dan Najeriya da ya hadiye sama da kilogiram 1 na hodar iblis samfurin Heroine da aka kukkula a cikin kororon roba tun daga jihar Lagos da nufin shigar da ita Aljeriya.

Shugaban kungiyar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta ADDENA Malan Ganda Saley, ya gargadi hukumomin kasashen biyu su hada gwiwa don toshe hanyoyin da masu fataucin myagun kwayoyi ke amfani da su.

Tu’ammali da myagun kwayoyi wata matsala ce da aka yi amince ta na barazana ga makomar matasa, dalili kenan kungiyoyi irinsu ONG Emergence Plus ke bada fifiko ga aiyukan waye kan al’umma game da illolin dake tattare da wannan mummunar dabi’a.

Bayanai sun yi nuni da cewa dimbin matasa ne ke cikin wannan harka ta miyagun kwayoyi a matsayin dillalai, lamarin da shugabar kungiyar ONG Kariyar Matasa, Hajiya Mounira Saliou ke alakantawa da jahilci da rashin aikin yi a wajen matasa.

Domin Karin bayani saurari rahotan cikin sauti:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like