Bayanai na ci gaba da fitowa game da harin kunar bakin waken da aka kai kusa da masallacin Manzo SAW da ke birnin Madina a kasar Saudiyya.
A kalla jami’an tsaro hudu ne suka rasa rayukansu da kuma dan kunar bakin waken da ya tayar da bam din.
Hotunan da gidan talabijin din kasar suka haska sun nuna wata mota na ci da wuta yayin da hayaki ya tashi sama da gawar mutane biyu a gefen masallacin.
Wannan na zuwa ne bayan kai wani harin kunar bakin wake masallacin mabiya darikar Shi’a da ke birnin Qatif a gabashin kasar, an kuma kai wani harin kusa da ofishin jakadancin Amurka da ke Jedda duk dai a ranar Litinin.
Kuma jami’an tsaro biyu ne suka mutu a harin na Jedda, kawo yanzu ba bu wata kungiya ko wanda ya dauki alhakin kai harin.
Tuni majalisar koli ta Malaman kasar suka yi Allah-wadai da harin, suna masu cewa, ”Maharan sun karya duk wata dokar tsarkakakken wajen.”
Har yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, sai dai an fi zargin kungiyar IS.
Masallacin Annabi SAW nan ne kuma inda kabarinsa yake.