Jami’an Tsaro Na Tabbatar Dokar Hana Zirga-Zirga A Birnin KanoGwamnatin jihar Kano ce ta sanya dokar a wani mataki na kare rayuka da dikiyar Jama’a.

Tun a ranar Lahadi yanayin tsaro a sassan jihar Kano ya shiga damuwa, bayan da hukumar zaben Najeriya ta fara tattara sakamakon zaben gwamna da ya wakana a ranar Asabar, al’amarin da ya sanya hukumomin tsaro suka tsaurara matakan tsaro.

Al’amura sun kara zafafa daga daren Lahadi zuwa wayewar garin Litinin, musamman gabanin hukumar INEC ta sanar da mutumin da ya yi nasara a zaben.

Comrade Mohammed Garba, shine kwamishinan labaru na Kano, ya ce la’akari da nauyin dake rataye wuyan gwamnati na tabbatar da aminci a tsakanin al’uma tilas ta dauki wannan mataki.

Ya ce tuni gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarni lallai a sanya hana zirga zirgar Jama’a, haka kuma gwamnati bisa hadin gwiwa da hukumomin tsaro na aiki tare domin ganin cewa, dokar ta yi aiki yadda ya kamata.

Masu murnar lashe zabe a birnin Kano

Masu murnar lashe zabe a birnin Kano

Sai dai ga alama matasa, musamman magoya bayan Jam’iyyar da ta yi nasara sunyi dandazo a titunan birnin Kano suna harkokin nuna murnar cin zabe.

Amma kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano Hussaini Muhammad, ya gargadi matasan da cewa su gudanar da harkokin su na murna cikin yanayi na kiyaye doka da oda. Yana mai cewa, Jami’an tsaro ba za su nade hannun su ba yayin da wasu ke yunkurin amfani da yanayin nuna murna su lalata dukiyar Jama’a.

Sai dai duk da haka, begen murnar dai ya sanya matasan lalata abubuwan amfani a galibin sassan birnin Kano, musamman allunan tallar hajar kamfanoni da alluna masu dauke da hotunan ‘yan siyasa da sauran ababe, duk kuwa cewa, an girke Jami’an tsaro a wurare daban daban na birnin Kano baya ga shawagin da jirgi mai saukar ungulu ke yi a sararin samaniyar birnin.

Domin Karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.Source link


Like it? Share with your friends!

1

You may also like