Jami’an tsaro sun harbe wani  riƙaƙƙen mai garkuwa da kuma kisan  mutane a jihar Rivers


Rundunar sojin Najeriya ta 6 dake Fatakwal ta yi bajekolin gawar riƙaƙƙen dan fashin nan, shugaban kungiyar asiri  kuma mai yin garkuwa da mutane wanda ake kira “Don Waney”.

Waney, yayi kaurin suna wajen kisa da kuma satar mutanen inda yake kai su wurin da yake aikata tsafe-tsafe.

Haɗin gwiwar jami’an tsaro da suka da sojoji daga rundunar sojin Najeriya ta 82 dake Enugu da kuma jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS sune suka samu nasarar kashe shi tare da wasu mutane biyu da yake tare dasu a wata musayar wuta da suka yi maboyarsa dake Enugu.

Hari mafi muni na karshe da ya kai shine a ƙaramar hukumar ONELGA ta jihar Rivers kan wasu mutane lokacin da suke dawowa daga coci bayan sun gudanar addu’ar musamman ta shiga sabuwar shekara.aƙalla mutane 23 ne suka mutu a harin.

Bayan ya aikata haka ne ya tsere inda ya koma Enugu ya cigaba da rayuwa tare da cigaba da shirin kai wani harin a ƙaramar hukumar ta ONELGA.

An dauko gawar Waney daga Enugu zuwa Fatakwal inda aka nunawa yan jaridu shi.

You may also like