Jami’an Tsaro cike da motoci 3 sun rushe sabuwar husainiyyah da ‘yan shia ke ginawa a garin Saminaka da ke jahar Kaduna a yau.
Haka kuma jami’an KASUPDA tare da rakiyar jami’an tsaro sun rusa muhallin makarantar mabiya shi’a wato Fudiyyah dake unguwar Babban dodo cikin garin Zariya.
‘Yan shi’an da dama dai na zargin gwamna El-Rufai da turowa a yi masu wannan rusau
Rahotanni sun nuna cewa bayan an rushe makarantar, jama’a sun yi ta kwasar kayayyakin dake cikinta suna awon gaba da su a matsayin ganima.
Ita kuma Husainiyyar dama an gina ta ne watanni biyu da suka gabata, don ci gaba da gudanar da tarurrukan mabiya Shi’a a Saminaka, kuma tun a lokacin wasu suka yi yunkurin tada rikici akan ginin, al’aamarin da ya sa gwamnatin Kaduna ta shigar da kara kotu, ita kuma kotu ta dakatar da ginin.
Rahotan ya kuma nuna cewa maganar har yanzu na kotu.
cc: ALummata