Jami’an tsaro sun sako Dino Melaye


Jami’an tsaro sun saki sanata Dino Melaye dake wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya a majalisar dattawa bayan da suka tsare shi da safiyar yau.

Jami’an hukumar shige da fice ta kasa ne suka kama shi da safiyar yau a filin jirgin saman Nmandi Azikiwe dake Abuja, lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa kasar Morocco.

Mai magana da yawun sanatan, Gideon Ayodele ya fadawa manema labarai cewa an saki sanatan bayan da suka shafe sama da sa’o’i biyu suna cece-kuce.

“An sake shi kusan awa daya da ta wuce,” ya ce.

” An sake shine bayan da yan sanda suka gaza dora masa laifin komai.”

A jawabin da ya wallafa a shafinsa na Twitter sanatan ya ce yana kan hanyarsa ta ziyarar aiki ya zuwa kasar Morocco da gwamnatin Najeriya ta dauki nauyi lokacin da jami’an tsaron suka kama shi.

You may also like