Jami’an tsaro sun yi wa gidan Dino Melaye kawanya


Dino Melaye, dan majalisar dattawa dake wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya yanzu haka yana makale a gidansa bayan da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS da kuma yan sanda sun yi wa gidansa dake unguwar Maitama a Abuja, kawanya.

Tun da fari Melaye ya wallafa wani sako a shafinsa na Twitter inda ya ce jami’an tsaro sama da 30 ne suka yi wa gidansa kawanya.

Ya kuma ce jami’an tsaro sun tsare dukkanin wata hanyar shiga ko fita da zata kai mutum ya zuwa gidan.

A safiyar yau ne dai jami’an hukumar shige da fice ta kasa suka kama shi a filin jirgin saman Abuja lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Morocco.

Sai dai sun saki dan majalisar bayan da ya shafe kusan awanni biyu a hannunsu.

Har ila yau jami’an tsaron sun kuma hana abokan aikinsa shiga gidan wandanda suka je domin nuna goyon bayansu gare shi.

You may also like