Jami’an tsaro sungano gawar Buharin Daji


Bayan ya shafe shekaru da dama yana addabar mutanen dake jihohin Katsina, Zamfara da kuma Kaduna a yanzu dai za a iya cewa ruwa ya karewa dan kada domin kuwa wani na hannun damansa ya harbe shi har lahira.

Wannan kasurgumin dan ta’adda ba kowa bane illa, Buharin Daji  mutumin da ya yi kaurin suna wajen satar shanu da kuma kai hare-hare kan kauyuka dake jihohin.

Buhari ya gamu da gamonsa bayan da ya sace shanun sirikin daya daga cikin na hannun damrsa da ake kira Dogo Gide, amma da Dogo ya nemi da a mayar da shanun sai Buhari ya nuna kin amincewa da haka.

Hakan ya sa Dogo ya bijire masa kafin daga bisani ya nemi su sulhunta.A waurin sulhun ne Dogo ya harbe Buhari tare da dukkanin mukarrabansa da ya zo da su.

Bayan ya kashe Buhari,Dogo ya sanar da jami’an tsaro inda gawarwakin su ke.

Tuni dai jamian tsaro suka dauke gawarwakin ya zuwa gidan gwamnatin jihar.

Abin jira a gani ko hakan zai kawo karshen kisan mutane da satar shanu a wadannan jihohin

You may also like