Jami’an Tsaron Masar Sun Hana Wani Jami’in Diblomasiyar Amurka Shiga Kasar


 

 

Gwamnatin kasar Masar ta hana wani jami’in diblomasiyar kasar Amurka shiga kasar don rashin mallakar Visar shiga kasar.

Kamfanin dillancin labaran ISNA a nan kasar Iran ya nakalto majiyar jami’an shige da fice a tashar sauka ta tashin jiragen sama na Alkahira yana fadar haka a safiyar yau Alhamis ya kuma kara da cewa tun shekara ta 2010 ne gwamnatin kasar ta kafa dokar hana duk wani dan diblomasiya na ko wace kasa a duniya shiga Masar ba tare da samun Visa shiga daga inda ya fito ba.

Banda haka majiyar ta kara da cewa a halin yanzu gwamnatin Amurka tana aiwatar da wannan dokar a kan dukkan Jami’an diblomasia da suke shiga kasar, har ma an taba zartar da wannan dokan wasu jami’an Jami’an diblomasiyar kasar Masar.

A jiya ne wani jami’in diblomasiyar kasar Masar wanda ke aiki a ofidhin jakadancin kasar a kasar Kenya ya shiga kasar Masar ba tare da Visa ba, da haka kuma doka ta hau kanshi aka maidashi daga inda ya fito.

You may also like