Jami’an tsaro a Najeriya sun kama wani dan jarida da ake zargi da alaka da Boko Haram a filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja babban birnin kasar.
Wani jami’an tsaro da ya nemi a boye sunansa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa, Ahmad Salkida ya isa Abuja a safiyar Litinin nan daga Dubai kuma yana sauka jami’an tsaro suka cafke shi.
Majiyar ta ce, ana ci gaba da bincikarsa kuma daga baya za a mika shi ga helkwatar rundunar sojin Najeriya.
A ranar 14 ga watan Agusta ne rundunar sojin Najeriya ta sanar da tana neman Salkida tare da wasu mutane 2 ruwa a jallo.
Sauran mutanen 2 su ne: Aishat Wakili da Ahmad Bolori.