Yan sanda sun ce sun sake kama sanata Dino Melaye, mai wakiltar mazabar yammacin Kogi a majalisar dattawa jim kadan bayan da wata kotu dake Abuja ta bayar da belinsa.
An kama Melaye a ranar Laraba bayan da kotu ta bayar da belinsa inda aka gurfanar da shi ana tuhumarsa da laifukan da suka hada da yunkurin hallaka kai, hada baki a aikata laifi da kuma lalata kayan gwamnati.
Kotun ta bayar da belinsa kan kudi naira miliyan ₦90 tare da kawo wasu mutane biyu da za su tsaya masa.
Sai dai kuma ana kammala zaman kotun jami’an yan sanda suka sake kama shi inda suka ce akwai sauran tuhume-tuhume da ake masa a wata kotu dake jihar Kogi.
A wata sanarwa da ya fitar mai magana da yawun rundunar yan sanda , Jimoh Mashood ya ce belin da aka bawa Melaye bai shafi laifin farko na dalilin da yasa aka kama shi