Jami’ar Ahmadu Bello Dake Zaria Ta Gina Matatan Man Fetur


Sashen Nazarin Sinidarai na Jami’ar Ahmadu Bello ya gina matatar man fetur mai karfin tace gangan daya a kowace rana.
Shugaban tawagar da suka gina matatar, Farfesa Ibrahim Muhammad Dabo ya nuna cewa za a rika amfani da matatar wajen horas da dalibai inda ya jaddada cewa sashen na da kwararrun da za su iya gina matatar da ta fi na Kaduna girma idan har gwamnati za ta mara masu baya.
Ya kara da cewa kashi 80 na kayyakin da aka yi amfani da su wajen aikin  duk a cikin gida aka samar da su kuma babu wani taimako daga kwararru na kasashen waje yana mai cewa an kashe Naira milyan 20 wajen kammala aikin.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like