Hukumar gudanarwar jami’ar Bayero dake Kano ta amince da korar wasu dalibai su 17 saboda samun su da rashin cika kaidar shiga makarantar.
Haka kuma an wanke wasu ddalibai uku saboda an gaza samun su da laifi.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da ke dauke da sa hannun shugaba da kuma sakatariyar kwamitin zartarwar na jami’ar dake lura da cika sharudan cancantar shiga jami’ar.
Sanarwar ta bayyana daliban da aka kora kamar haka:
1. Yahaya Shuaibu Muhammad
2. Khadija Ibrahim
3. Yusuf Usman Abdullahi
4. Mansura Muhammad Danjuma
5. Sumayya Said Ismail
6. Ado Auwalu Malam
7. Aliyu Musa
8. Aminu Muhammad Usman
9. Ibrahim Aminu Dahiru
10. Surajo Ahmad Adamu
11. Aliyu Haruna
12. Nuruddeen Yunusa Kuta
13. Anas Abdullahi Muhammad
14. Nusaiba Ado Gwarjo
15. Idris Kawuwa
16. Saidu Araga Ahmed
17. Rafatu Abdulkareem
” Dalibai ukuAbdulmajid Sale, Mahmud Danladi and Yusuf Abdulmateen, an wanke su daga laifi bayan da kwamitin gaza gano kuskure a takardun na shiga makarantar,” sanarwar tace.