Kwamitin zartarwar jam’iyar ACPN ya rushe kwamitin gudanarwar jam’iyar a wasu jihohi biyar jihohin sune Kwara, Osun, Anambra, Borno da kuma jihar Benue kan zargin cin amanar jam’iya.
Ganiyu Galadima shugaban jam’iyar ta ACPN na ƙasa wanda ya yi magana da ƴa
Da yake magana da ƴan jaridu a hedikwatar jam’iyar dake Abuja ya kuma sanar da sake kafa kwamitin riko na shugabancin jam’iyar a jihar Kwara ƙarƙashin jagorancin Issa Aremu.
Ganiyyu yace korarren shugaban jam’iyar na jihar Osun ya goyi bayan ɗan takarar jam’iyar APC a zaɓen kananan hukumomi na kwanannan da aka gudanar a jihar.
Shugaban ya cigaba da cewa yayin da suke shiryawa tunkarar zaben shekarar 2019 dole ne suyi duba da irin mutanen da basa can basa ma’ana mutanen da basa taɓuka komai a jam’iyar dole ne mu sallame su.