Jam’iyar APC Reshen Jihar Katsina Ta Dakatar Da Mataimakin Shugaban Jam’iyar  


Reshen jam’iyar APC na jihar Katsina ya dakatar da mataimakin shugaban jam’iyar mai lura da Shiyar Katsina ta Tsakiya, Alhaji Mamman Yaro Batsari.

Tuni wani taron shugabannin jam’iyar na jiha ya amince da dakatarwar da akayi masa kana aka kafa wani kwamitin bincike mai mutane biyar da zai binciki zarge zargen da ake masa na cin amanar jam’iya.

Kwamitin da Barista  Yarima Danja zai shugabanta an bashi sati biyu da ya mika rahotonsa ga kwamitin zartarwar jiha na jam’iyar.

Sauran yan kwamitin sun hada da Barista  Auwal Adam Bindawa, Barista Muktar Daura, Barista Lawal Ayuba da kuma Lawal Adamu a matsayin sakatare.

Lokacin da aka tuntubeshi don jin tabakinsa,Batsari yace yanzu ba lokacin da yadace yayi magana bane domin har yanzu kwamitin bai tuntubeshi ba. 

 Abinda jam’iyar tayi kuskure ne  ta yaya zasu kafa kwamiti sannan kuma suyi gaban kansu su dakatar dani ba tare da sun jira kwamitin ya kammala aikin da aka bashi ba ,” Ya koka. 

” A iya sanina ban san abinda ake zargina da aikatawa ba, ba a fadamin na aikata komai ba,” yace. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like