Jam’iyar APC Zata Iya Koyon Darasai Daga Kayin Da Tasha A Zaben Cike Gurbin  Sanata Da Akayi A Jihar OsunMinistan harkokin wajen kasarnan Geoffrey Onyeama, yace akwai darasi da jam’iyar APC yakamata ta koya daga kayin da dankararta yasha a zaben cike gurbi na Sanata da aka gudanar ranar Asabar a Jihar Osun.

Ademola Adeleke dan takarar jam’iyar PDP shine ya samu nasara a zaben da kuri’u 97,480 yayin da Mudashiru Hussain dan takarar jam’iyar APC wanda yasha kayi,ya samu kuri’u 66,116.

Ademola kanine ga marigayi Sanata Isiaka Adeleke,Sanatan dake wakiltar mazabar yammacin Osun kafin rayuwarsa a ranar 23 ga watan Afirilu.

Da yake magana bayan wata ganawa da yayi da John Oyegun shugaban jam’iyar APC na Kasa, Onyeama yace  jam’iyar tana bukatar yin aiki tare. 

“Ana koyon darasai daga komai, wani lokacin ana iya koyon darasi daga rashin yin nasara, fiye da yadda zaka koya lokacin da kayi nasara,” ministan yace. 

“Ina tunanin akwai kyawawan darasi da yakamata mu koya , da suka hada da wajen tsarawa, da kuma zama tare cikin ko wacce jiha, da kuma kaucewa yanayin da zaisa wani mutum yakeji yafi kowa muhimanci.

” A matsayinmu na jam’iya,dole mu hadaka kai,muyi aiki tare,bawaI mutum daya zamu duba ba a’a makomar jam’iyar yakamata mu kalla. ”

  A cewarsa sun tattauna rikicin da ake fama dashi a reshen jam’iyar na jihar Enugu da kuma hanyoyin da za a magance shi. 

Yace a matsayinsa na mai rike da mukamin gwamnati mafi girma a jihar, alhakinsa ne ya tabbatar cewa rikicin bai yi tsamari ba. 

 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like