Jam’iyar PDP a jihar Benue ta dakatar Ayu







Jam’iyar PDP reshen jihar Benue ta sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu kan zargin yiwa jam’iyyar zagon kasa.

Takardar dakatar da Ayu mai dauke da kwanan watan 25 ga Maris na dauke da sahannun mutane 12 dake shugabantar mazabar Igyorov dake karamar hukumar Gboko ta jihar inda Ayu ya fito.

A cikin wasikar shugabannin sun yi zargin cewa Ayu ya yi wa PDP zagon kasa a mazabar a lokacin zaɓuka da aka yi na 2023.

Har ila yau jam’iyyar ta zargi Ayu da kin halartar zaɓen gwamnoni da na yan majalisun jihohi na ranar 18 ga watan Maris.






Previous articleI won’t run away from EFCC, will honour their invitation – Wike




Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like