Sabon rikici na neman rikita jam’iyar PDP reshen jihar Kano kan shirin zaɓen sabon shugaban jam’iyyar.
Jaridar Daily Trust ta gano cewa bayan korar tsohon shugaban jam’iyyar, Alhaji Rabi’u Dan Sharu, PDP ta shirya zaɓe domin cike gurbin da ya bari.
Yan takarkaru biyar da suka hada da Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa, Muhammad Rabi’u Sabo Bakin Zuwo, tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Alhaji Gambo Sallau, Alhaji Aminu Sa’ad Beli da kuma Alhaji Aminu Maraya Barkum sune aka ce sun nuna sha’awar su ta ɗarewa kujerar shugabancin jami’iyar.
Amma kuma daya daga cikin yan takarar, Aminu Sa’ad Beli ya yi korafin cewa jam’iyar na shirin dora Doguwa a matsayin sabon shugaban jam’iyyar.
“Wasu daga cikin iyayen jam’iyar suna kokarin kakabawa ya’yan jam’iyyar Doguwa a matsayin shugaba, na rubuta korafi zuwa ofishin uwar jam’iya ta kasa inda nake adawa da wannan shirin,” ya ce.
Beli yace yana jiran amsar da uwar zata bashi kafin yasa matakin da zai ɗauka anan gaba.
Da jaridar ta tuntubi mai magana da yawun jam’iyar a jihar, Alhaji Musa Danbirni yaƙi yarda yace komai game da batun.