Jam’iyar PDP Ta Dakatar Da Ifeanyi Uba 


Jam’iyar PDP ta sanar da dakatar da Ifeanyi Uba shugaban kamfanin Capital Oil & Gas daga jam’iyar.

A wata sanarwa da kwamitin shugabancin rikon jam’iya na kasa yafitar tace an dakatar da Uba, ne saboda zargin da yakewa jamiyar kan yadda ta gudanar da zaben fidda gwanin dan takarar da zai wakilci jam’iyar  a zaben gwamnan jihar Anambra da za a gudanar a watan Nuwamba mai zuwa. 

Haka kuma jami’iyar ta bukaci karin bayani daga wurin Sanata Buruji Kashamu, kan shigar da kansa wani batu a reshen jam’iyar na jihar Ogun. 

 “Kwamitin riko na jam’iyar a yau, yana sanar da dakatar da Ifeanyi Uba kan kalaman batanci da kuma zargi marar tushe akan yaya da kuma wasu dattawan jam’iya,” sanarwar tace. 

“Uba yayin da yake nuna rashin gamsuwarsa da matakin da kwamitin rikon jam’iya  na kasa  ya yanke game da zaben fidda gwani na dantakarar da zai yiwa jam’iyar takara a zaben gwamnan Anambra,kwamitin daukaka kara ya tabbatar da Oseloka Obaze a matsayin halattaccen dan  takara, tun daga wannan lokacin Ifeanyi Uba,  yake yin wasu kalamai masu cike da zargi akan shugabancin jam’iyar.”  

“haka kuma jami’iya ta bukaci karin bayani daga wurin Sanata Buruji Kashamu kan shigarsa cikin wani rikici a reshen jam’iyar na jihar Ogun.”


Like it? Share with your friends!

0

You may also like