Jam’iyar PDP Ta Kara Rasa Kujera A Majalisar Dattijai


​Jam’iyar PDP,ta kara rasa kujera daya a majalisar dattijai, bayan da shugaban kwamitin kudi na majalisar,  Sanata John Enoh, daga jihar Kuros Riba, ya sauya sheka zuwa jam’iyar APC. 

Enoh ya bayyana sauya shekar da yayi, a zaman majalisar na jiya Talata, wanda Shugaban Majalisar Bukola Saraki ya jagoranta. 

Sauya shekar da yayi yasa kujerun jam’iyar PDP sunyi kasa zuwa 41,yayin da na abokiyar hamayyata APC, sukayi sama zuwa kujeru 67.

Canza shekar tasa yakawo, hayaniya a zaman majalisar, yayin da yayan jam’iyar PDP suka rika cewa “jeka,” su kuwa takwaransu na APC tashi sukayi daga kujerunsu domin karbar Enoh zuwa cikinsu. 

Sai dai Sanata Emanuel Bwacha,daga jihar Taraba ya bayyana Enoh,  a matsayin, mai yawon shakatawar siyasa,yace a shirye suke da su karbeshi idan ya dawo


Like it? Share with your friends!

0

You may also like