Jam’iyar PDP Tayi Kira Da A Janye Sojoji Daga Yankin Kudu Maso Gabas 


Jam’iyar PDP tayi kira ga gwamnatin tarayya da ta janye sojojin da aka tura zuwa yankin kudu maso gabas kana ta fara tattaunawa da mutanen yankin don kaucewa faruwar rikici anan gaba. 

A wata sanarwa,sakataren yada labaran jam’iyar, Dayo Adeyeye, yace  yan kasa nada yancin  su bayyana abinda suke bukata  kamar yadda doka ta tanada bai ci ace an dakatar dasu da karfin soja ba. 

“PDP ta bayyana cewa a wannan lokaci da zukata suke dada baci tattaunawa maimakon rikici  itace kadai mafita bawai fada ba itace kadai mafita wajen warware rikicin yankin kudu maso gabas dama na sauran sassan Najeriya baki daya. 

“Abinda kasarnan ke bukata a yanzu bai wuce yanayin zaman lafiya ba, wanda idan babu shi baza a iya samun cigaba ba a kowanne bangare, amma kuma abinda yake faruwa a yankin kudu maso gabas yankin da wani bangare ne mai muhimmanci na Najeriya, babu tantama zai kawo nakasu a kokarin da dukkaninmu muke nakai Najeriya zuwa wani matsayi na cigaba.”  


Like it? Share with your friends!

0

You may also like