Shugabannin jam’iyyar APC na kasa a jiya Alhamis sun gargadi ma’aikatan su dake sakatariyar jam’iyyar da su daina rokon kudi daga wurin bakin da suke kawo ziyara sakatariyar.
Shugabannin jam’iyyar sun bayyana hakan ne a yayin wani taro da suka yi da ma’aikatan da suke aiki a sakatariyar jam’iyyar dake Balantyre Street, Wuse 2, Abuja.
Shugabannin sun sha alwashin daukar kwakkwarar mataki ga duk ma’aikacin da aka kama da laifin haka.
Wata majiya daga wurin taron ta bayyana cewa shugabannin jam’iyyar sun nuna rashin jin dadinsu game da hakan kasancewar suna karbar manyan bakin ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, jami’an diflomasiyya daga ciki da wajen kasar nan.
A kwanakin baya dai wasu daga cikin ma’aikatan na jam’iyyar APC sun nuna rashin jin dadin su kan yadda al’amuran jam’iyyar ke tafiyar hawainiya tare kuma rashin ba su albashi akan lokaci.