Jam’iyyar APC ta Lashe Zaben Jahar Edo


godwin-obaseki

 

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta bayyana dan takarar APC a zaben gwamnan jahar Edo, Mista Godwin Obaseki a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan.

Obaseki wanda ya kawo kananan hukumomi 13 a cikin 18 da ke jahar, ya samu kuri’a 319,484 yayin da dan takarar PDP, Osagie Ize-Iyamu ya samu kuri’a 253,173, ya kuma kawo kananan hukumomi 5.

Sai dai jam’iyyar PDP ta jahar ta yi watsi da sakamakon inda ta ce an yi magudi a cikinsa.

A wani taron manema labarai, shugaban jam’iyyar PDP a jahar Dan Orbih ya bayyana cewa ba su yarda da sakamakon ba tunda abunda hukumar ta bayar ya sha bam bam da abunda wakilansu suka kawo masu daga mazabu 192 a fadin jahar da banbancin kusan 30,000.

A dan haka ne suka ki sanya hannu a takardar sakamakon.

 

cc: Alummata

You may also like