Jam’iyyar APC Tace Zatayi Raddi Kan Wasiƙar IBB Idan Buƙatar Hakan Ta Taso


Jam’iyyar APC ta bayyana cewa za ta yi raddi ga wasikar da Tsohon Shugaban Kasa, Ibrahim Badamasi Babangida ya rubutawa Shugaba Buhari bayan ta kammala nazarin wasikar wanda a ciki ya nemi Buhari ya bari sabbin jini su ci gaba da jan ragamar mulkin.

Sakataren Yada Labarai na APC, Bolaji Abdullahi ne ya yi wannan ikirarin inda ya nuna cewa har yanzu ba su karanta wasikar ba don haka a cewarsa, idan akwai bukatar yin raddi, jam’iyyar za ta bayyana matsayinta kan korafe korafen da tsohon Shugaban ya zayyana a cikin wasikar.

You may also like