Jam’iyyar Musulmi ta lashe zaben ‘yan majalisa a Maroko


 

 

Jam’iyyar masu da’awar Muslunci a Maroko ta lashe zaben ‘ya majalisar dokoki da aka gudanar a jiya Jumma’a a kasar inda ta samu kujeru125 daga cikin kujeru 395 da majalisar ta kunsa

Marokko Parlamentswahl - Regierungspartei PJD, Abdelilah Benkirane (Reuters/Y. Boudlal)

Jam’iyyar masu da’awar Muslunci a Maroko ta lashe zaben ‘ya majalisar dokoki da aka gudanar a jiya Jumma’a a kasar inda ta samu kujeru125 daga cikin kujeru 395 da majalisar ta Kunsa a sakamakon da hukumar zaben kasar ta bayyana a wannan Asabar.

Babbar abokiyar hamayyarta ta PAM wato Parti Authenticite et modernite wacce  Ilyas El Omari wani mashawarcin Sarki Mohammed na biyar ya kafa a shekara ta 2008 na a matsayin ta biyu da kujeru 102, sannan jam’iyyar Istiqlal tsohuwar jam’iyya ta mazajen da suka yi gwagwarmayar samar da ‘yancin kasar ta Maroko na a matsayin ta uku da kujeru 37.

Jam’iyyar Musulmi ta PJD wato Parti Justice et Developpement wacce ake kwatantawa da jam’iyyar ‘yan uwa Musulmi ta masar ita ce daya dayar jam’iyar masu siyasar da’awar Muslunci da ke rike da gwamnati a duk fadin duniyar Larabawa.

Kuma sakamakon wannan zabe ya ba ta damar kara kafa sayunta a fagen siyasar kasar ta Maroko inda sarki ke a matsayin shugaban kasa kana jagoran Musulmi wanda amma kuma shi ne ke da wuka da nama kan manufofin kasa dangane da harakokin tsaro da tattalin arziki da kuma diplomasiyar kasa da kasa.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like