… Babu wata nasara da aka samu na kakkabe Boko Haram, duk farfaganda ce, inji Gwamna Fayose
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa nasarar kakkabe ‘yan Boko Haram daga dajin Sambisa.
PDP ta ce ta jinjina wa Buhari bisa tsayuwar dakan da ya yi a yakin da ake yi da ‘yan Boko Haram.
Haka kuma jam’iyyar ta nuna farin ciki kan abin da ta ce ci-gaba da Buhari ya yi a kan kokarin da gwamnatin Goodluck Jonathan na PDP ta yi a yakin da ta’addanci.
Wata sanarwar da sakataren watsa labaran jam’iyyar Price Dayo Adoyeye ya fitar ta ce nasarar da aka samu a yakin da ake yi da Boko Haram ta samo tushe ne daga irin kokarin da gwamnatin baya ta yi, musamman ‘yan makwanni, gabanin gudanar da zaben shuugaban kasa a shekarar 2015.
Sanarwar ta PDP ta kuma jinjina wa sojojin Nijeriya bisa jajircewa a yukurin raba kasar da masu tada kayar baya.
To sai dai PDP ta ce kwace dajin Sambisa ba ya nufin cewa an kammala yaki da ta’addanci, ta yi kira hukumomin Nijeriya su matsa-kaimi wajen kakkabe ‘yan ta’adda daga dazukan kasar da dama da suka zama wata mafaka ga ‘yan ta’adda.
Ba kasafai dai PDP ke yabawa Buhari ba, kuma a lokuta da dama tana caccakarsa kan koma baya a bangaren tattalin arziki.
A gefe daya kuma, Gwamnan jihar Ekiti Peter Ayodele Fayose ya ce, farfagandar da jam’iyar APC ta saba ce na cewa an kawo karshen mayakan Boko Haram a dajin sambisa.
Fayose ya ce ba wai matsalar Boko Haram ce kadai ba ke ciwa ‘yan Nijeriya tuwo a kwarya ba, ya ce ko baya ga Boko Haram akwai matsaloli da dama da jama’a ke bukatar gaggawa.
Fayose ya kuma yi kira ga shugaba Buhari da ya kawo karshen matsalar tattalin arziki da kuma bakar yunwar da ke galabartar da ‘yan Nijeriya kafin ya yi murnar samun ci gaba cikin mulkinsa.
Gwamnan ya kuma kara da cewa bikin kirsimeti na bana ya zama mafi muni a tarihin Nijeriya. Ya ce har yanzu jama’ar kudu maso yamma ba su gani a kasa ba, balantana su yi Allah san barka.