Jam’iyyar PDP Ta Zargi Jam’iyyar APC Da Shirin Yin Magudi A Babban Zabe A Jihar Neja
Jam’iyyar ta PDP ta ce ta gano yadda jam’iyya mai mulki ta APC ke bin yankunan karkara na jihar Neja tana karbar katinan zabe daga hannun jama’a ta basu kudi ko ta yi masu alkawalin wata alfarma.

To sai dai jam’iyyar APC ta yi watsi da wannan zargi inda ta ce ba shi da tushe balle makama.

Hon. Yahaya Ability, shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar PDP mai kula da sashe na uku a jihar Neja, ya ce suna da hujjoji masu karfi akan wannan korafi kuma tuni suka gabatar da su ga hukumar zaben Najeriya.

To sai dai kakakin jam’iyyar APC a jihar Neja Musa D. Sarkin Kaji ya ce wannan bayanin ba gaskiya bane. Ya kara da cewa ‘yan PDP na so ne kawai su tallata hajarsu amma su sani cewa hukumar zabe mai zaman kanta ce, bata bangaranci.

Sai dai jami’in hulda da jama’a na hukumar zaben Nigeria mai kula da jihar Neja Usman Kuta Abubakar, yace basu da labari kan batun amma zasu gudanar da bincike daga nan su dauki matakin da ya kamata.

Ya zuwa yanzu dai hukumar zaben na ci gaba da fadakarwa akan jama’a su je ofisoshin hukumar zabe da ke yankunan karkara domin karbar katin zabensu.

Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like