Jam’iyyu 10 Muka Yiwa Rijista –  INEC


Hukumar zabe ta kasa wato INEC ta yiwa jam’iyyu 10 rijista, wanda sakamakon wannan rijistar ya zama yanzu ana da jam’iyyu 40 a Kasar. A baya kafin wannan rijistar, jam’iyyu 30 ake da su. Hukumar ta wallafa wannan bayanin ne a Shafin yanar gizo-gizonta. Sannan ta tabbatar da cewa jam’iyyun da aka yiwa Rijistar sun hada da; Better Nigeria Progressive Party (BNPP), Democratic Alternative (DA), Masses Movement of Nigeria (MMN), National Action Council (NAC) and National Democratic Liberty Party (NDLP).
Da kuma sauran jam’iyyun da suka hada da; Nigeria Elements Progressive Party (NEPP), National Unity Party (NUP), Nigeria Peoples Congress (NPC), Peoples Progressive Party (PPP) and Peoples Redemption Party (PRP).
Mr Nick Dazang, shi ne mataimakin Daraktan Sanin Zabe da hulda da jama’a ya bayyana cewa; wadannan jam’iyyun 10 da aka yiwa Rijista suna daga cikin jam’iyyun da aka soke riistarsu a baya. Sai dai hukumar ta zaben ta bi Umurnin Kotu ne wajen sake yi musu Rijista bayan daukaka karar da aka yi ba a cimma nasara ba. Hukumar ta zaben ta sake tabbatar da rijistar su ne a ranar 1 ga watan Satumban wannan shekarar.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like