Jam’iyyun Adawa Ba Zasu Samu Nasara Ba A Zaben 2019 – Sanata WammakoSanata Aliyu Magatarkada Wammako mai wakiltar Arewacin jihar Sokoto a majalisar Dattijai ya bayyana cewa, jam’iyyar APC za ta ci gaba da samun wurin zama a jihar Sokoto ba gudu ba ja da baya, in da ya ce kuri’u kalilan jam’iyyun adawa za su samu a zaben 2019.

Sanatan ya bayar da tabbacin sa da kuma lamuni akan cewa har yanzu kan jam’iyyar APC a jihar a hade ya ke, domin kuwa ba bu wata tangarda a tattare da ita.

Wammako ya bayyana hakan ne a jihar ta Sokoto yayin karba da taya murna ga wanda ya yi nasarar cin zaben jam’iyyar APC a mataki na farko na zaben dan malajisar mai wakiiltar mazabar Kware da Wammako, Alhaji Ahmed Kalambaina, shugabannin jam’iyyar reshen jihar da kuma sauran masu ruwa da tsaki.

A kalamansa ya ke cewa, “jihar Sokoto za ta samu kuri’u masu yawa a zaben 2019, fiye da yadda ta samu a zaben 2015, saboda a shekarar 2015, wasu jam’iyyun adawar sun dan yi mana kutsu, amma cikin yarda ta Ubangiji hakan ba zai faru a

You may also like