Jam’iyyun Siyasa Su Yi Kokarin Fitar Da ‘Yan Takara Masu Amana Da Kishin Kasa-Buhari


4bhf6a7ce4fe92oam_800c450

 

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana cewa shuwagabannin siyasa nako wacce jam’iyya a Nijeriya su yi kokarin fitar da mutane na gari masu gaskiya da rikon amana da adalci tare da kishin kasa.

 

Shugaba Buhari ya ci gaba da cewa “Irin wadannan mutane ya kamata a ringa zakulowa wajen basu damar jagorantar al’umarsu a dukkan matakai na shugabanci tun daga kan kansila har izuwa shugaban kasa musamman a zabe mai zuwa na shekara 2019.

 

Saboda wannan ita ce hanya dodar ta kakkabe tarin matsalolin kasarmu Nijeriya tare da habakar tattalin arzikin kasa da samun zaman lafiya Mai dorewa a tsakanin al’umar Nijeriya masu banbance banbancen addini da yare da kuma shiya-shiya wanda Allah ya hadamu a guri daya a karkashin Nijeriya.

 

Saboda zalunci da rahin adalci da karancin masu kwatanta gaskiya da rikon amana a cikin shuwagabanni jagororun jama’a yana haifar da karayar tattalin arzikin kasa tare da samar da kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasa.

You may also like