Jammeh ya fara gudun hijira a kasar Equatorial Guinea


 

 

Tsohon shugaban Gambiya Yahya Jammeh ya fice daga kasar da ya yi mulki na tsawon shekaru 22, a wani mataki na warware rikicin siyasa da kasar ta Yammacin Afirka ta tsinci kanta a ciki.

Ex-Präsident Jammeh verlässt Gambia (Picture-Alliance/dpa/J. Delay)

Mutumin da tun farko ya ki sauka daga mulki duk da kaye da ya sha a zaben ranar 1 ga watan Disamba, Jammeh ya yi sanadiyyar tayar da jijiyar wuya da yunkurin daukar mataki na soji domin tilasta shi bawa sabanon shugaba Adama Barrow madafan iko.

Tsohon shugaban na Gambiya tare da rakiyar shugaba Alpha Cone na Guinea sun bar birnin Banjul a wani karamin jirgin sama zuwa Conakry babban birnin Guinea, kana daga bisani ya shige kasar Equatorial Guinea, inda zai yi zaman gudun hijira, a cewar shugaban kungiyar ECOWAS Marcel Alain de Souza a birnin Dakar.

You may also like