Jamus na son Chaina ta sa baki | Labarai | DW



Babban jami’i a ma’aikatar harkokin wajen Jamus Andreas Michaelis ne ya bayyana a yayin wata ganawarsa da manzo na musamman na kasar Chaina a lokacin da ya yada zango Berlin, a ci gaba da zagayen wasu kasashen Turai, kafin ya isa a birnin Moscow.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamus Christian Wagner, ya ce a tsawon tattaunawarsu da Li Hui, takwaransa na Jamus ya nanata batun dakatar da yakin a Ukraine, inda Jamus na son ganin Chaina ta yi amfani karfin fada ajin da ta ke da shi ga gwamnatin Moscow da ta jingine makamai. 





Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like