Jamus na son horas da matasa sana’o’i | Labarai | DWShugaban gwamnatin na Jamus Olaf Scholz ya bayyana haka ne a lokacin gangamin bikin ranar ma’aikata da ya gudana a birnin Koblenz da ke yammacin kasar.

Wannan kira na shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da Jamus ke fama da karancin ma’aikata, lamarin da ya kai wasu kamfanoni da neman ma’aikata ruwa a jallo, to sai dai ana ganin wasu dokokin kasar na hana kwararun ma’aikata daga wasu kasashe shigowa kasar domin cike gurbin da suke da shi.

Shugaban gwamnatin ya kara da cewar karancin ma’aikata da kasar ke fama da shi na mai zama barazana ga makomarta a nan gaba.

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like