Janar Babangida Zai Aurar Da ‘Yar AutarsaTsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida zai aurar da diyarsa Halima a ranar Juma’a mai zuwa a garin Minna babban birnin jihar Neja.

Halima Babangida ita ce ta biyu a ‘ya’ya mata da Janar Babangida ya haifa kuma ita ce ‘yar auta a dukkanin ‘ya’yansa.

 

‘Ya ce ga marigayiya Maryam Babangida. Kuma an haife ta ne a lokacin da Babangida yake jagorancin mulkin Nijeriya a jihar Lagos a tsakanin 1985 zuwa 1991 kafin a dawo da birnin tarayya Abuja.
Sunan angonta Auwal Lawal Abdullahi, wanda yake rike da saurautar Sarkin Sudan Gombe. Dan kasuwa ne.
Za a daura auren ne a gidan tsohon shugaban kasan dake Hilltop Villa a garin Minna da misalin karfr 2:30 na rana.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja, Zubairu Mu’azu ya bayyana cewa kimanin jami’an ‘yanda dubu hudu za a baza a kan babban titin Minna da kuma manyan hanyoyin cikin birnin domin tabbatar da tsaro a yayin daurin auren.

You may also like