Janar-janar ɗin da ke rikici don mallakar Sudan.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Janar Mohamed Hamdan Dagalo (a hagu) da Janar Abdel Fattah al-Burhan (a dama)

Karar tashin bama-bamai, da turnukewar bakin hayaki a sararin samaniya, da fargaba a kullum da zaman rashin tabbas a yayin da ruwan harsasai da makaman rokoko da kuma jita-jita ke bazuwa.

Rayuwa a Khartoum babban birnin kasar Sudan da sauran sassan kasar da dama ta kara tabarbarewa fiye da kima.

A tsakiyar wannan dambarwa akwai janar-janar din soja biyu: Abdel Fattah al-Burhan, shugaban rundunar sojin kasar ta Sudan (SAF), da Mohamed Hamdan Dagalo, da aka fi sani da Hemedti, jagoran dakarun da ba na gwamnati ba (RSF).

Duka biyun sun yi aiki tare, kana suna gudanar da wani juyin mulki tare – yanzu yakin neman karfin iko na yin kaca-kaca da kasar ta Sudan.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like