Janye sojoji daga Dapchi shi ya jawo BH suka kai hari garin -Gwamna Geidam 


Gwmnan jihar Yobe Ibrahim Geidam ya ce janye dakarun soja da aka yi daga Dapchi shi ne ya buɗe kofar kai hari akan makarantar sakandare ƴan mata dake Garin.

Gwmnan ya ce ko sati ɗaya ba a yi ba da janye sojoji daga Dapchi ƴan ta’addar suka kawo harin.

Geidam ya bayyana haka a ranar Lahadi lokacin da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a Damaturu babban birnin jihar.

Jumullar ɗalibai mata su 110 aka rawaito an sace a makarantar bayan da ƴan ta’adda suka kai hari a makarantar ranar Litinin.

“Na ɗora alhakin laifin kai harin Dapchi akan sojoji da kuma ma’aikatar tsaro ta kasa  waɗanda suka janye sojoji daga garin.

“Harin ya faru ne kusan mako guda da janye sojoji daga Dapchi.

“Kafin haka Dapchi na cikin zaman lafiya babu wani lamari makamancin haka da ya taɓa faruwa. Amma mako daya kacal baya ɗauke sojoji Boko Haram suka kawowa garin hari.

 Ya kwantanta lamarin da yafaru da kuma harin da aka kai a makarantar sakandare ta  Buni Yadi inda aka kashe wasu dalilbai da dama. 
Ya ce da akwai sojoji a wurin to da dukkanin hare-haren biyu basu faruba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like