Jarirai Guda 18 Aka Tsinta a Garin Funtua Cikin Watanni 4


baby-factory

 

Daraktan ilimi da walwalar jama’a na karamar hukumar Funtua, Ibrahim Nasir ya bayyana cewa a cikin watannin 4 da suka gabata kawai, an tsinto jarirai 18 da ransu a karamar hukumar.

Ya bayyana haka ne a jiya Laraba yayin da yake magana da jaridar Premium Times, inda ya ce lamarin ya zama ruwan dare a karamar hukumar.

Ya ce akan tsinto jariran ne a makwararrun ruwa, Juji, kwata da gidajen da ba’a gama gininsu ba.

A fadarsa, ko a shekaran jiya (24 ga wata), sai da aka tsinci wata jaririya a wata tsohuwar shadda.

 

Ya kara da cewa yanzu haka jariran na samun kulawa, kuma har wasu sun nuna sha’awar karbar su, sai dai ya ce ana kokarin cika sharudodi kafin a mika jariran gare su.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like