Jaruma Nafisa ta karbi lambar yabo a birnin London


Shararriyar jarumar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta samu nasarar zama jarumar da tafi kowacce jaruma a Kannywood.

An dai gudanar da bikin bayar da kyautar a birnin London ranar Asabar jarumi Ali Nuhu da Ramadan Booth na daga cikin jaruman da suka halarci bikin.

“Kyauta ta 16 kenan … Ina kirgawa,”jarumar ta rubuta a shafinta na twitter.

Jarumar da ta fito a fina-finai da suka shahara kamar su ‘Guguwar So’, ‘ Ya Daga Allah’, Dan Marayan Zaki  da sauransu.

Jarumar ta bayyana cewa duk da cewa ba wannan ne karo na farko ba da take karabar kyauta amma wannan kyautar na da muhimmanci sosai a gare ta.

You may also like