Jarumar Wasan Fim Din Hausa Rabi Isma’il Da Aka Yankewa  Hukuncin kisa Ta Sake Shiga Komar Jami’an TsaroJami’an hadin gwiwa na hukumar ‘yan sandan ciki da na kula da gidan yari, sun sake kama jarumar wasan fina-finan Hausar nan wadda ta tsere daga gidan yarin Hadejia a watan Disemban shekara ta 2011.

Jarumar, wadda ta ke da lambar k/22c Rabi Isma’il a lokacin da take gidan yari, an yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya ne a babban kotun jihar Kano, bayan an kama ta da laifin kashe wani saurayinta a 2005.

Jarumar dai tana gidan yarin a Kaduna, amma daga bisani aka canja mata gidan yari izuwa Kano, inda daga nan ne ta tsere shekaru 6 da suka gabata.

Majiyarmu ta ce, a 2012, kutun koli, ta kara tabbatar da hukuncin babban kutun, bayan ta kama Rabi Isma’il da laifi da ake zarginta da shi dumu-dumu a shekara ta 2011, inda aka ce ta kashe saurayin mai suna Auwalu Ibrahim ne don ta mallaki kadarorinsa.

Shugaban hukumar kula da gidan yari, ya bayyana farin cikinsa, tare da jinjina ga jami’an hukumar ‘yan sandan ciki da ma ‘yan sanda da suka kama wannan mai laifin.

Ya bukaci al’umma da su ci gaba da ba su ingantattun bayanai ga wadanda suka gudu daga hannun hukuma da ma ‘yan ta’adda ga jami’an tsaro.

Inda ya tabbatar da cewa, duk wanda ya gudu kuma yana ganin ya boye, to ko a jima ko a dade zai shiga hannun hukuma kuma.

You may also like