” Ina farin cikin halartar wannan taron saboda ya kara ba ni karfin guiwa kan yadda jihar Adamawa ta yi gaban kanta wajen kaddamar da shirinta na yaki da rashawa kuma ta fito da salonta da za ta yi amfani da shi don neman shawarwarin al’ummar kasa.
Idan ba a manta ba, a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2015, a lokacin da aka rantsar da ni, na jaddada cewa kasar nan na fuskantar manyan kalubale na rashin tsaro da cin hanci da rashawa kuma na yi imanin cewa idan muka hada kai za mu kawo karshen wadannan manyan kalubalen.
Kamar yadda na yi hasashe, a yau Ina alfahari kan nasarorin da muka samu a bangaren yaki da rashawa. Duk yake a karkashin tsarin mulkin tarayya da muke amfani da shi, gwamnatin tarayya ba ta ikon yin katsalanda kan yadda jihohi ke tafiyar da harkokinsu amma kuma yadda ake ci gaba da fallasa cin hanci da rashawa duk daga matakin kananan hukumomi yana matukar faranta mani rai.
Za mu ci gaba da sa ido na tabbatar da gwamnatoci masu adalci tun daga matakin karamar hukuma zuwa tarayya. Na gamsu matuka kan matakan da Gwamantin Adamawa ke dauka wajen samar da ababen more rayuwa ga al’ummarta wanda wata hanya ce na dakile kafofin cin hanci da rashawa.
Ina kira ga wasu gwamnonin jihohi kan su yi koyi da Adamawa wajen inganta harkokin ci gaban kasar nan. Ayyukan da na gani a Yola sun ba ni karfin guiwa kan kyakkyawar makomar jihar kuma Ina fatan hakan zai ci gaba dorewa. Ina jinjinawa gwamnatin Adamawa kuma Ina yabawa Al’ummar jihar kan goyon bayan da suke ba gwamnati kuma Ina kira gare su kan ci gaba.”
Ina godiya kuma Allah Ya Albarkaci Nijeriya.
*
— Shugaba Muhammad Buhari
( Buhari ya gabatar da wannan jawabin ne a yau Talata a lokacin da ya bude taron koli kan yaki da rashawa wanda gwamnatin Adamawa ta shirya)