Jawabin Shugaba Buhari na Zagayowar Ranar ‘Yancin Kai. 


Shugaba Muhammad Buhari ya tabbatar wa al’ummar Nijeriya cewa gwamnatinsa tana aiki tukuru wajen ganin ta farfado da tattalin arzikin Nijeriya inda ya nuna cewa sun rigaya sun gano bakin zaren matsala kuma sun tanadi hanyoyin warware su a cikin tsanaki.
Ya kuma yaba wa ‘yan Nijeriya bisa hakuri da juriya da suka nuna a cikin wannan yanayi na kunci inda ya ce yana sane kan irin halin da ake ciki a gidajen al’umma na yunwa amma kuma ya jaddada cewa Babban manufarsa ita ce na sake dora kasar kan turba madaidaiciya.
Ya kara da cewa yanayin tattalin arziki ya janyo wasu iyaye ba sa iya biyan kudin makarantar ‘ya ‘yansu yayin da wasu iyayen abin da za su ci yana gagararsu sai kuma matasa da suka rasa ayyukan yi bayan kammala karatu sai kuma ‘yan kasuwa da ke fama da rashin ciniki.
A cewarsa, a duk tsawon rayuwarsa yana karbar albashi don ya san halin da  magidanci ke fuskanta yayin da albashinsa bai isa wajen biya masa muhimman bukatun rayuwa yana mai cewa a cikin kasar nan akwai mutane da dama da ke sadaukarwa kan wannan yanayi.
Ya ce, dalilin da ya sa ya tsaya takarar shugabancin kasa har sau hudu shi ne don ya tabbatar da cewa an samu gyara a kasa ta yadda za a daina satar kudaden gwamnati wanda hakan ya janyo aka kasa samar da ayyukan raya kasa, tsaro, kiwon lafiya, ilimi da kuma ayyukan yi.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa wannan halin da ake ciki ba zai taba dorewa ba yana mai cewa kada al’ummar kasa su rudu da mafita ta gaggawa wadda ba za ta dore ba yana mai cewa a kan haka ne ya dage don ganin an samu maslaha ta dindindin.

You may also like