Bayan kammala Zaben Kananan Hukumomin da aka gudanar a Jihar Kano, a ranar 10 Ga Fabarairu, 2018, an rika samun rahotanni, musamman a soshiyal midiya, inda aka rika zargin cewa kananan yara da shekarun su ba su kai munzilin jefa kuri’a ba, sun dangwala a wurare da dama yayin zaben. Zargi da hasashen da aka rika yi a lokacin, shi ne ai tunda dai Rajistar Sunayen Masu Zabe da aka yi amfani da ita, ta INEC ce, to ana ganin kamar ita INEC din ce tun da farko ta yi wa kananan yaran rajista kenan.
Tilas a nan na jaddada muku cewa har yau babu ko mutum daya da ya kawo wani korafi ga INEC dangane da wannan zabe. Amma sai ga shi duk da haka, wasu masu ruwa da tsaki, ciki har da wata jam’iyyar siyasa sun shiga kafafen yada labarai su na sukar INEC, abin har ma ya kai su ga yin tababar sahihancin sunayen masu Rajistar Zabe da INEC ta yi wa rajista.
Saboda INEC ta damu sosai da irinn zarge-zargen da wasu ke yi dangane da rajistar sunayen, sai hukumar ta kafa kwamitin bincike a ranar 21 Ga Fabarairu, 2018, domin gano shin ko akwai sunayenn kananan yara a cikin rajistar da INEC ta bai wa Hukumar Shirya Zaben Jihar Kano (KANSIEC), kamar yadda doka ta tanadar.
To bari na fara da tantance muku cewa babu ruwan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da shirya zaben Kano. Abu daya da doka ta wajibta wa INEC shi ne damka wa KANSIEC rajistar sunayen wadanda ta yi wa Rajistar Zabe a jihar, kuma hakan kawai ta yi. Shirya zabe da gudanar da shi a jihar Kano, duk aikin hukumar zaben jihar ce, wato KANSIEC, wadda kuma karkashin jihar ta ke, ba a karkashin INEC ba.
Abu na biyu kuma, jama’a su fahimci cewa INEC ba ta kafa kwamitin binciken ta wai don ya binciki yadda KANSIEC ta gudanar da zaben ta na Kananan Hukumomin Kano, ko don gano matsalolin da aka fuskanta a lokacin zaben ba. INEC a dokance ma ba ta da ikon yin haka. Kawai abu daya ne aikin Kwamitin Bincken da INEC ta kafa. Aikin kuwa shi ne ya gano shin ko akwai sunayen kananan yara a cikin Sunayen Rajistar Zabe wanda INEC ta bai wa KANSIEC, ko a’a?
Wannan kwamitin bincike kuwa ya kunshi Kwamishinan Zabe Na Kasa, Injiniya Nahuce a matsayin Shugaba, Kwamishinonin Yanki biyu, Barista Mike Igini da Kassam Geidam, da kuma wasu Daraktoci da ma’aikaikatan Hukumar, wadanda kwararru ne wajen zakulo binkike a na’urori. Kuma tuni kwamitin ya gabatar da rahoton sa. INEC ta yi nazarin rahoton kwamitin a tsanake, kuma ta gamsu da sakamakon rahoton kwamitin. Dama kuma Abubuwa Hudu ne aka ce Kwamitin Binkice ya maida hankali a kan su, wadanda kuma a kan su ne rahoton kwamitin ya bayyana kamar haka:
i. Hukumar Zaben Jihar Kano ta bukaci INEC ta ba ta sunayen Rajistar Zaben Jihar Kano, kuma an ba ta domin ta gudanar da zabe. Sai dai kuma a wurare kalilan ne aka yi amfani da Rajistar. Ashe kenan ba a yi amfani da wannan Rajista ta INEC a rumfunan zabe da dama ba. Zancen gaskiya ma ba a yi amfani da Katin Shaidar Rajista (PVC) ba.
ii. Tunda har ba a yi amfani da Rajista ta INEC wajen tantance masu dangwala kuri’a ba, to ashe kenan idan har yara kanana sun jefa kuri’a, sun jefa ne ba tare da sunayen su ya na cikin Rajistar Sunayen Masu Zabe ta INEC ba. Sannan kuma INEC ta yi nazarin wasu hotunan kananan yaran, kuma ta tabbatar da cewa sun dade ana yada su a soshiyal midiya tun kafin Zaben Kananan Hukumominn Jihar Kano.
iii. Akwai bukatar hadin kai tsakanin INEC da sauran masu ruwa da tsaki a harkar zabe, a rika bibiyar da inganta Rajistar Zabe ta Kasa, domin kakkabe wadanda bas u cancanta su yi zabe a cikin ta ba, ciki kuwa har da bukatar cire sunayen matattu a ciki.
iv. Ya kamata INEC ta yi aiki tare Hukumar Zabe ta Jihohi (SIEC), domin tabbatar da inganta zabuka a Najeriya.
Da yake babban abin da ya fi daukar hankali ga Hukumar Zabe da ‘yan Najeriya a nan shi ne Rajisatar Zabe ta Kasa, saboda ita ce ginshikin zaben 2019, bari na yi muku wani takaitaccen bayani dangane da rajistar zaben da mu ke da ita a halin yanzu.
Wato rajistar da mu ke da ita a yanzu, tun wadda INEC ta tattara ce a cikin 2011. Idan za ku iya tunawa, kafin zaben wannan rajista cike ta ke da kurakurai da wasu sunayen da za ku rika ji da gani bambarakwai, kamar Mike Tyson. Wato kamata ya yi a ce rajistar zaben 2011 ta na dauke da shaidar yatsan kowane mai rajista, to Hukumar Zaben da ta gabata ta gano cewa babu alamomin yatsun wasu da yawan masu rajista, wasu kuma alamar yatsan na su ya yi dishi-dishi. Banda wannan kuma an samu inda jama’a da dama su ka yi rajista sau biyu. To wadannan matsaloli ne hukumar zaben lokacin ta yi kokarin magancewa, har ta yanke shawarar fara sabuwar rajista a cikin 2011.
Tun bayan kammala zaben 2011, hukukmar zabe ta ci gaba da inganata wannan rajista ta hanyoyi uku da dokar kasa ta bada iznin yi. (i) Ta hanyar kara sabbin sunayen wadanda ake yi wa rajista ta yau da kullum (CVR); (ii) bin diddiginn tantance shaidar yatsan wanda ya yi rajista domin gano wadanda suka yi rajista sau biyu a cire su. (iii) Gyaran sunayen da ba su cika ba, ko sunayen da ba a rubuta daidai ba, da kuma tantance inda shaidar yatsan hannu ba su kammala ba.
Wannan kuwa ya zama abu mai muhimmanci, musamman shigo da tsarin Katin Zabe na Dindindin, PVC da kuma na’urar tantance sahihancin katin zabe (SCR). Da wannan dalili ne duk wani rakod da babu shaidar yatsun mai rajista sai da aka tanatance shi, idan kuma ba a yi haka ba, to wasu masu zabe ba za sun iya yin zabe da tsarin amfani da PVC da SCR ba.
Sakamakon wannan gyare-gyare da tantance-tantance ne aka samu tantagaryar rajistar sunayen masu zaben 2015 da ya gabata suka kai mutane milyan 68,833,476.
Saboda haka, wannan Hukumar Zabe ta yi amanna da cewa ta gaji rajistar zabe mai kamar haka:
i. Wadda ta kunshi cikakken tsarin yi wa jama’a rajista. Domin sai da ta kai ma wasu kasashe sun rika zuqa sun a daukar irin salon tsarin da INEC ta bi ta tattara sunayen masu rajista tare da killace sunayen. Misali, a lokacin da aka gudanar da zaben Shugaban Kasa a Liberiya, Hukumar Zaben Kasar ta bi ta hannun Majalisar Dinkin Duniya, ECOWAS da kuma Kungiyar Shugabannin Hukumomin Zaben Kasashen Afrika ta Yamma, ECONEC, wadda ni ne shugaban ta, su ka roki yin amfani da wasu ma’aikatan INEC domin su warware musu wasu hardaddun bayanai a cikin rajistar sunayen masu zaben kasar. An yaba sosai da irin ingantaccen aiki kuma sahihi da ma’aikatan mu suka yi musu, musamman ganin yadda aka samu nasarar gudanar da zaben.
ii. Wadda ta kunshi sunayen masu rajista milyan 68.8, wadda kuma ita ce rajistar da ta fi saura yawan jama’a da aka taba yi a zabukan can baya.
iii. Wadda sunayen da ke cikin ta sun yi daidai da shaidar yatsun wadanda suka yi rajista.
iv. Wadda ta jibinci amfani da katin PVC ta hanyar tantancewa da na’urori.
v. Wadda aka tabbatar ana ci gaba da bibiyar ta ana inganta ta ta hanyar Cigaba da Rajista a Yau da Kullum, kamar yadda doka ta tanadar. A karkashin Hukumar Zabe ta yanzu, an samu karinn masu rajistar zabe 432,233 daga kan sunayaen da ke cikin rajistar 2015. Daga Afrilu 2017 lokacin da muka fara Cigaba da Rajistar Zabe (CVR) zuwa watan Disamba da ya gabata, mun kara yi wa mutane milyan 3,981,502 rajista
Yan a kuma da muhimmanci mu tunatar da jama’a cewa wannan Rajistar Masu Zabe ta Kasa an yi amfani da ita a zaben 2011 da na 2015, da ma wasu zabukan cike-gurbi da dama da suka biyo baya. Wadannan zubukan da suka biyo baya kuwa, bayan an tabbatar da cewa sunn kai gejin duk wani sahihancin zabe da duniya ke bukata, sun kuma samar da sakamakon zabuka ga jam’iyyu daban-daban, ba tare da nuna son kai ko magudi ba.
Tabbas, Rajistar da aka yi Zaben Kananan Hukumaomin Jihar Kano a ranar 10 Ga Fabrairu, 2018, ita dai ce aka tattara tun a zaben 2011, aka inganta ta a 2014, sannan aka yi amfani da ita a zaben 2015. Wannan Hukuma ba ta kara ko da suna daya tal a cikin wannan rajista ba. Da ita dai ce aka yi duk zabukan baya da ‘yan siyasa wasu su ka yi nasara, wasu kuma su ka fadi zabe.
Saboda haka abin al’ajabi ne matuka a yau kuma a wayi gari wasu har su fito su na cewa wannan rajista, wacce da ita ce suka ci zabe a baya ko suka sha kaye kuma suka amince da shan kaye, kuma su fito su ce rajistar ba abin yarda da sahihancin ta ba ce.
Bari na kara jaddada cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Ta gamsu da cewa a yanzu mu na da rajistar zabe wadda za mu iya dogara da ita, kai ko ma da a ce ba ta inganta 100 bisa 100 ba. Mun kuma yi amanna da cewa wannan rajista wata babbar kadara ce mai matukar muhimmaci ga kasar nan, kuma ita dai ce wani sahihin rumbun da ake tutiya da shi a fadin kasar nan, wanda ke dauke da kididdigar wasu adadin ‘yan Najeriya da suka haura milyan 70. Kuma ta ke dauke da sunayen su, adireshin su, hotunan su, shaidar yatsun hannayen su goma da kuma lambar tarho din su da ma sauran wasu bayanai dangane da su.
Ina jan hankalin daukacin ’yan Najeriya da su kalli wannan babbar kadara da kasar nan ta mallaka da matukar muhimmanci. Mu hadu a taimaka a kara inganta ta domin mu kara tabbatar da an tsame dukkan dan abin da ya rage a cikin ta, na daga sunayen da ba su cancanta ba.
Yanzu kuma bari na sanar da ku abin da mun ke kan yi da wanda mu ke shirin yi domin ci gaba da bibiya da inganta wannan rajista da cire sunayen da ba su cancanta ba a cikin ta.
Na Farko: Mun maida aikin ci gaba da yin rajista a kullum fiye da yadda aka taba yi a baya. Domin tun daga cikin watan Afrilu, 2017 ake yi, kuma ba za a daina ba, har sai zabe ya rage saura kwanaki 60. Mu na kuma lika sunayen wadanda suka je suka yi rajista, domin a sake tantancewa ko da mai wani korafi. Wannan kuwa ya na daukar wasu kwanaki 5 zuwa 14. Muna kira ga ’yan Najeriya da a koda yaushe su yi amfani da wannan dama su rika gaggauta sanar da INEC dangane da sunayen wadanda ba su cancanci yinn rajista ba, har ma da kananan yara wadanda suka yi rajista idan ma akwai su. Har da bakin-haure da kuma bayanan da aka cike ba daidai ba, ko wadanda ba su kammalu ba.
Na Biyu: Kamar yadda doka ta tanadar, mu na ci gaba da bai wa jam’iyyun siyasa kwafe-kwafe na rajistar da mu ka yi a kowace shekara, da kuma kafin zabe da kuma kowane zaben gwamna da aka gudana ba a lokacin zaben-game-gari ba. Kai kwanan nan ma a ranar 28 Ga Fabrairu, 2018, mun damka wa kowace jam’iyya daga cikin jam’iyyu 68 da mu ke da su, muka ba su sunayen mutane milyan 3.9 da muka yi wa rajista a cikin 2017. Mun kuma yi kira a gare su da su yi amfani da wannan rajista domin su samu dama da saukin isa zuwa ga masu jefa kuri’a. sannan kuma su ma za su iya bincikawa domin su ga shin ko akwai sunayen wadanda ba su cancanta ba a ciki, domin su gaggauta sanar da INEC.
Amma abin takaici, tun daga lokacin da aka kaddamar da Hukumar nan a 2015, har yau babu wata jam’iyya ko guda daya da ta taba zuwa ko sau daya ta kawo mana rahoton samun wasu sunaye ko sunan wani wanda bai cancanta ba a cikin rajistar sunayen masu zabe da muka damka musu.
Na Uku: Mu na aiki kafada-da-kafada tare da Hukumar Kula da Shige-da-fice ta Najeriya, domin tsane sunayen bakin-haure daga cikin rajista, wadanda ba su cancanci jefa kuri’a a Najeriya ba. Sannan kuma sun yi alkawarin tura jami’an su a wuraren sabunta rajista da tantancewa don gane bakin-haure.
Na Hudu: Mun yi niyyar amfani da jama’ar da ke yankin da mu ke da Wuraren Yin Rajista 8,809 ko Mazabu, ta hanyar Jami’an Aikin Rajista (RAOs). Mun samar da wani kundin tattara bayanai ga wadannan jami’ai. Mu na kira ga ‘yan Najeriya da su ba su kwakkwaran hadin kai domin tantance wadanda ba su cancanta su yi rajista ko zabe ba, domin a cire sunayen su.
Na Biyar: Mun kudiri aniyar yin amfani da fitattun kungiyoyin sa-kai da sa-ido da kafafen yada labarai wajen buga sunayen masu rajista a nan gaba. Dokar Kasa Sashe na 20 da aka yi wa kwaskwarima cikin 2010, ta ce a rika buga ilahirin sunayen wadanda suka yi rajista akalla kwanaki 30 kafin ranar zabe. Don haka mu na fatan su ma kungiyoyin nan da kafafen yada labarai za su taya mu sa-idon gano wadanda ba su cancanci yin rajista ba a cikin sunayen.
Na Shida: Bayan kammala aikin cigaba da rajista da ake kan yi, watau sai ana sauran kwanaki 60 a fara zaben da za a fara a ranar 16 Ga Fabrairu, 2016, ya kamata kowa ya sani cewa za a daina kafin saura kwanaki 60 ga zabe, mun yi niyyar lika sukayen dukkan masu rajista a kowace shiyyar da kowa ya yi rajista. Wannan ma zai sake bayar da wata damar tantancewa ko gano wadanda ba su cancanta ba. Domin a cire sunayen su.
Na Karshe: INEC ta gamsu da rahoton Kwamitinn Nahuce, inda ya bada shawarar Hukumar ta hada kai da masu ruwa da tsaki domin kara inganta zabe a Najeriya, har da Zabukan Kananan Hukumomi a kasar nan. Dama tuni INEC na da kyakkyawar alaka da Kungiyar Hukumomin Zabe na Jihohi (FORSIECON). Kuma za mu ci gaba da yin haka. Cikin wasu hanyoyin da za mu kara bi shi ne taimakawa a kara inganta hukumomin zabe na jihohi ta yadda za su inganta daidai da yadda tsarin zabe na kasa da kasa na duniya ya kai ga inganci.
Sain dai me, akwai wani karin haske dangane da wannan zargi na yin amfani da kananan yara a Zaben Kananan Hukumomin Jihar Kano. Ya bai wa INEC wata damar sake duba Rajistar Sunayen Masu Zabe tare da amfani da masu ruwa da tsaki a harkar zabe sake dubawa domin a kara inganta ta, musamman wajen tsame sunayen da ba su cancanci yin rajista ba.
Kamar yadda ko yaushe mu ke yi wa ‘yan Najeriya alkawari, mu na yin marhabin da kowace irin suka ko gyara mai ma’ana, za kuma mu rika karbar shawarwari ko gyaran da aka yi wa kura-kuran mu, a inda duk ya zama wajibi mu yi hakan. Mu na yin kira da ‘yan Najeirya su kalli aikin INEC cewa ba na Hukumar ba ce ita kadai, na mu ne gaba dayan mu.
Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).