Duk da rikicin rabuwar kawuna da ya mamaye jam’iyyar APC mai mulki a yayin zabukan shuwagabanninta da aka yi a kwanan nan, hedikwatar ta fitar da jerin sunayen wadanda suka yi nasarar samun mukaman shugabancin jam’iyyar a jahohin su.
Sai dai da yawa daga cikin ‘yan lelen jiga-jigan yan jam’iyyar ba su samu nasara ba kamar yadda aka yi tsammani.
Misali, wanda shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya fitar ya buge wanda ministan yada labarai, Lai Muhammad ya fitar. A jahar Lagos, wanda Bola Tinubu Ke so shi ya doke wanda bangaren Fouad Oki ya fitar.
Ga jerin sunayen:
- Abia- Donatus Nwankpa
- Adamawa- Ibrahim Bilal
- Akwa Ibom- Ini Okopido
- Anambra- Emeka Ibe
- Bauchi- Uba Ahmed Nana
- Bayelsa- Jonathan Amos
- Benue- Abba Yari
- Borno- Ali Dalori
- Cross River- Godwin John
- Delta- Cyril Ogodo
- Ebonyi- Eze Nwachukwu
- Edo- Anslem Ojezua
- Ekiti- No Congress
- Enugu- Ben Nwoye
- Gombe Nitte Amangal
- Imo- Hillary Eke
- Jigawa- Ado Sani Kiri
- Kaduna- Emmanuel Jekeda
- Kano- Abdullahi Abass
- Katsina- Shittu Shittu
- Kebbi – Bala Sani Kangiwa
- Kogi- Abdullahi Bello
- Kwara- Ishola Balogun Fulani
- Lagos- Tunde Balogun
- Nasarawa- Philip Shekwo
- Niger- Muhammed Liman
- Ogun- Dikia Adebisi
- Ondo- Ade Adetimehin
- Osun- No Congress
- Oyo- Akin Oke
- Plateau- Letep Dabang
- Rivers- Ojukaye Amachree
- Sokoto- Isa Achida
- Taraba- Abdulmumini Vaki
- Yobe- Adamu Chilariye
- Zamfara- Lawal Liman and
- FCT – Abdulmalik Usman