JIFATU Ya ‘Yantar Da Daurarru 150 Daga Gidajen Kurkuku


jifatu (1)

 

 

A yayin da wasu kamfanoni ke yin rige-rigen neman ribar zahiri na kasuwanci, shi kuwa kamfanin rukunonin Jifatu da ke da sassa daban daban a kasar nan, karkashin Shugabancin Manajan Daraktan Kamfanin na Kasa – Alhaji Sabitu Muhammad Yahya (Jifatu), ya jagoranci kamfanin wajen aikata aikin lada don samun riba mai tsoka a duniya da lahira.

Nazarin musamman da wakilinmu a Kano ya yi, ya nakalto mana cewa Jifatu ta biya makudan kudade ga wasu mutane da aka daure sakamakon kaddara, ko kuma basussuka da ake binsu, suka gaza biya saboda halin rayuwa na yau da kulllum a gidajen kurkuku daban-daban a nan kasar. Hakan wani babban yunkuri ne wajen tabbatar da muradun kamfanin ya fito fili daidai yadda aka tsara, kamar yadda jami’in tsare-tsaren kamfanin, Alhaji Nafi’u Shu’aibu Koki ya tabbatar.  An bayyana fito da daurarrun daga gidan yari da kuma sauran tsare-tsaren duk bisa irin tausaya wa al’umma ta fannoni daban-daban wanda Jifatu kanyi akai-akai.  Alhaji Koki ya fadi haka ne a lokacin da yake ganawa da wakilin namu a babban ofishin kamfanin na kasa dake birnin Kanon Dabo a makon da ya gabata.

Jami’in wanda yayi magana da yawun shugaban rukunonin Jifatu na kasa, Alhaji Sabitu Yahya Muhammad, inda ya ce “Wannan tallafi na ‘yanto da Fursunoni, wato daurarru daga kurkuku ya samo asali ne tun kimanin shekaru uku da su ka wuce, a sakamakon tunani da hangen nesa na Alhaji Sabitu Yahya Muhammad Jifatu na kyautatawa al’umma da tausaya musu ta fuskar ilimi, lafiya da kuma samawa dimbun matasa aikin yi ta hanyar koya musu kasuwanci, sana’a da kuma ba su jari gwargwadon iko a burinsa na ciyar da al’umma gaba. Wannan shi ne muradin shugaban namu, doomin samun ci gaban Kano da ma kasa gabaki daya, wanda hakan ne ta janyo irin gudummawar da kamfanin Jifatu, karkashin shugabancinsa da ke Kano,” in ji shi.

Wakilin namu ya bayyana cewa su dai wadannan daurarru da kamfanin jifatu ya ‘yantar da su a karshen watan Ramadan da ya gabata su ne kamar haka daurarru daga yarin Gwauron- Dutse da Kurmawa su ne guda 40, inda suka lankwame kudi kimanin Naira Dubu 500. Na kano kawai sai kuma na jihar Katsina su 39, wanda su ma suka lankwame kudi da bai kasa dubu 500 ba. Sai kuma jihar Bauchi guda 35 su ma naira dubu 500 haka kuma kamfanin Jifatun ya kai irin wannan agaji na ‘yantar da daurarru Jihar Zamfara inda aka yantar da daurarru guda 32 domin dai albarkacin watan Ramadan,  inda daurarru kimanin 150 su ka samu shakar iskar ‘yanci daga kurkuku daban-daban kamar na Kano, Katsina, Bauchi, Zamfara.

Haka kuma bayan biya musu tara akan abin da ya kaisu kurkuku kamar bashi da kuma kananan laifuffuka da suka kasa biyan tarar da kotuna suka yanke musu a lokuta daban-daban wanda yanzu kamfanin Jifatu ya biyamusu ankuma basu kudin mota kamar naira 3000 da za su shiga mota su koma ga iyalansu a wurare daban-daban.

Jami’in ya kara da cewa, sun yi la’akari da wanda kkaddara ta fada musu na bashi ko kuma wani abu mai kama da haka amma dai duk masu kananan laifuffuka ne a ka biya musu tarar suka fita bisa tsarin da doka ta tanada a yi, don haka ya yi amfani da wannan dama wajen yin nasiha ga wadanda suka samu wannan ‘yanci daga kurkuku, su yi amfani da damar da suka samu wajen zaman su ga sun zama  mutane na gari su zama masu bin doka da oda da kuma tashi su nemi na-kansu, su guji abin da zai sake kawo su wannan wuri mara dadin zuwa ta hanyar yi wa ‘yan’uwansu gargadi da shawarwari ta yarda za a samu bin doka da zaman lafiya a kasa dama duniya baki daya.

You may also like