Jihar Adamawa ta tallafawa mutanen da ambaliyar ruwa ta ritsa dasu


Gwamnatin jihar Adamawa ta tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta soma shafa a jihar da kayayyakin tallafi, yayin da gwamnan jihar ke gargadin wadanda ke zaune a bakin kogin Binuwai da su sauya wuraren zama ganin cewa kasar Kamaru ta soma sako ruwa daga madatsar ruwan Lagdo.
Ya zuwa yanzu dai tuni ruwan da aka sako da ga madatsar ruwan Lagdo dake jamhuriyar Kamaru ya fara isowa, kuma kamar yadda tun farko ma hukumomin kula da yanayi da bada agaji suka yi gargadin cewa a bana akwai yiwuwar samun ambaliyar ruwa.

Kuma yanzu haka tuni wasu al’ummar jihar Adamawa dake zaune a bakin kogin Benue suka fara fuskantar barazanar ambaliyar ruwan, lamarin da ke tayar da hankalin mahukunta a jihar, da yake gargadin al’ummar jihar Adamawa, gwamnan jihar Sanata Mohammadu Bindo Umaru Jibrilla, ya gargadi mutanen dake zaune a bakin kogi da su kwashe kayansu su bar yankunan.

Sai dai a kwai al’umomin bakin kogin da ke kokawa da cewa gwamnatin jihar bata cika alkawarin da ta yi musu ba na basu guraren da zasu zauna, duk kuwa da cewa an basu takardu sun cika sun biya fiye da shekaru Uku.

You may also like