Jihar Bauchi Ce Kan Gaba A Yawan Wadanda Suka Yi Rijista A Shirin Gwamnatin Tarayya Na N-Power. Kididdiga ya nuna cewa a shirin da gwamnatin tarayya ta samar don tallafawa matasa (N-Power), jihar Bauchi ce kan gaba a yawan wadanda suka yi rijista, inda jihohin Lagos da Rivers suke biye da ita.
Nasarar hakan baya rasa nasaba da samar da cibiyoyin yin rijistar kyauta a dukkanin kananan hukumomin jihar da gwamnatin jihar karkashin jagorancin Barista Muhammad Abdullahi Abubakar ta yi.
Nan ba da jimawa ba za a fitar da jerin sunayen wadanda suka yi rijistar. Kimanin mutane dubu dari biyu da suka yi rijistar ne za a baza a su a jihohin kasar nan a rukunin farko. Sannan kuma tuni gwamnatin jihar Bauchi ta ware makarantun sakandire guda biyar a cikin birnin jihar domin horar da wadanda za a horar. Inda kowane daga cikin wadanda aka dauka za su dinga samun naira dubu talatin a duk wata a matasyin albashi. Kuma za a samar musu kayan aiki wanda zai taimaka musu.
Haka kuma ofishin bunkasa harkokin ci gaban al’umma za su yi hadin gwuiwa da ma’aikatar SUBEB wajen horar da wadanda aka dauka a fannin koyarwa, yayin da kuma ma’aikatar gona ta jihar za ta horar da wasu daga cikin su a fannin gona wasu kuma ma’aikatar bunkasa harkar lafiya za su dauke su a fannin kiwon lafiya. Daga karshe kowannen su za su iya ci gaba da aiki a fannoni daban-daban da aka horar da su da zarar sun samu kwarewa.
Nan ba da jimawa ba za a fitar da jadawalin sunayen wadanda za a soma horarwa a rukunin farko (wadanda adadinsu ya kai dubu biyar) da  kuma jadawalin wadanda suka yi rijistar a jihar Bauchi baki daya.
Gwamna Barista Abubakar ya samu yabo daga ciki da wajen jihar kan samar da cibiyoyin yin rijistar shirin kyauta da ya yi a dukkanin kananan hukumomin jihar wanda hakan ne ya baiwa matsan jihar damar yin rijista a shirin. Haka kuma daga cikin wadanda suka yi nasarar hayewa a shirin sun fito ne daga dukkanin kananan hukumomin jihar.

You may also like