Jihar Bauchi tare da hadin gwiwar Asusun kula da kananan yara wato UNICEF ta kaddamar da shirin kariya ga rayuwar al’uma tare da bada tallafin kudi a garin Luda da ke karamar hukumar Bauchi.
Manufar shirin shi ne kara karfafa wa Iyaye mata gwiwa domin su rika zuwa awu tare da rika kai yaran su rigakafi a kan kari don rage mutuwan yara da Iyaye a lokacin haihuwa. Bugu da kari babban burin wannan shiri shi ne yakar cututtuka irin Foliyo daga jihar Bauchi.
An fara kaddamar da wannan shiri ne a uguwanni uku a kowace karamar hukuma daga cikin Bauchi, Misau da Katagum tare da zimmar fara magance matsalar daga nan.