Jihar Filato Za Ta Fara Fitar Da Dankalin Turawa Zuwa Kasashen Waje


A kokarinta na samar da karin hanyoyin shigar kudade da habaka tattalin arzikin jihar tare da bunkasa noma, gwamnatin jihar Filato ta bayyana fara fitar da Dankalin Turawa zuwa kasashe waje a shekara mai zuwa.

Da yake karin haske ga manema labarai a Jos, Gwamnan jihar Simon Bako Lalong ya ce, “jihar Filato tana da yanayi mai kyau wanda ake bukata domin samar da Dankalin Turawa mai yawa wanda har zai isa a fitar da shi zuwa kasashen ketare”.

“Fitar da dankalin zai samar mana kudin shiga da muke bukata domin yin ayyukan raya kasa da kuma samawa matasa aikin yi ganin sune kashin gadon bayan kowacce al’umma”.

Daga karshe Gwamna Lalong ya yi kira ga matasa da su hada hannu domin samar da zaman lafiya ga kasa tare da kama sana’a komai kankantar ta, don samun abin dogaro da kai.

You may also like