Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kaduna ta tsayar da ranar 30 ga watan Disamba a matsayin ranar da zata gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar.
Shugabar hukumar Saratu Binta Dikko wacce tayi wannan sanarwa jiya A Kaduna tace sanar da ranar zaben na nufin za iya fara gangamin yakin neman zabe a jihar.
Tace hukumar ta saka lokacin da jam’iyu zasu gudanar da zaben cikin gida daga ranar 10 ga watan Oktoba zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba.inda ta kara da cewa ana sa ran za a kammala yakin neman zabe a ranar 29 ga watan Disamba.
Tayi roki masu ruwa da tsaki, jam’iyun siyasa da yan takarkarunsu da su girmama doka da kaucewa yin kalaman ta da hankali da kuma rikici.
“Yan takara dole ne su girmama muhallin mu ta hanyar tabbatar da cewa hotunansu da sauran kayan yakin neman zabe basu mata mana kyakkyawan muhallinmu na jihar Kaduna ba.
“Wadanda suke fatan su zama shugaban cemu bai dace a ce sun zama mutanen da basa girmama muhallinmu ba, “tace.