Jihar Kano Ta shiga Hannu Nagari A Karkashin Gwamnatin Ganduje –  Tambuwal 


Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakoncin takwaransa na jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da tawagarsa a fadarsa da ke birnin Sokoto a jiya a Alhamis.
Tawagar ta hada da mataimakin shugaban jama’iyya ta kasa na shiyyar Arewa maso yamma, Alhaji Inuwa Abdulkadir da shugaban jama’iyyar APC ta jihar Kano Abdullahi Abbas, Sanata Barau I Jibril, Bashir Usman Tofa da manyan iyayen jama’iyya da masu rike da mukaman Gwamnati.

You may also like